An fara hadayar Missa da misalin karfe 10:00 na safe.
Kungiyar mawaka (Catholic Choir) ne suka raira waka shiga.
Mai girmama Bisho, Fadodi, sistoci, Katikist, Mass servers sun yi jerin gwano (procession) zuwa cikin Ikilisiya har zuwa kan olta kamar yadda aka saba yi a Ikilisiyar Katolika.
Mai girma Catholic Bishop na Katsina ne ya jagoranci Hadayar Missa. Inda aka fara, ya yi jawabin gabatarwa. Inda ya ce wannan Missa ta na muhimmanci kwarai da gaske a Ikilisiyar Katolika, domin ana gudanar abubuwa masu muhimmanci kamar:
Gudanar da Hadayar Missa
Sabunta alkawarin da Fadodin mu suka dauka lokacin da aka nada su
Albarkatar mayukan da muke amfani da su cikin shekara da sauran abubuwa masu masu muhimmanci.
Choir sun sun raira wakar Ubangiji ka yi jinkai da daukaka
Karatu 1: Ishaya 61:1-3, 6, 8-9
Maimaicin Zabura
Karatu 2: Wahayin Yahaya 1:5-8
Bishara: Luka 22:14-23
Wa'azi: Mai Bishop na Ikilisiyar Katolika ta Katsina ya yi wa'azin. Ya ce akwai tsakanin Crism Mass na wannan shekara da na shekarar da ta gabata. Saboda bara an shi da Cathedraticum na Katsina Deneary. Bishop ya ce wannan Missa ta Fadodi ce da Saura jama'ar Ikilisiya (Lay faithful). Saboda ya kamata a kowanne Parish da ke karkashin wannan Diocese wakilai sun kasance da yawa. A cikin wannan Hadayar Missa ana albarkatar mayukan da mu ke amfani da su domin yin Baptism, shafewar marasa lafiya, a Ikilisiyar Katolika. Rana biyu tafi muhimmanci a rayuwarmu; ranar da aka haife mu, ranar mutuwarmu. Ma'aurata na daukar alkawarin za su zauna tare cikin dadi ko akasin haka, a ranar da suke bikin cika wadansu shekaru na aurensu suna sabunta alkawarin da suka daukarwa juna. Haka ma Fadodi a wannan rana su ma su na sabunta alkawarin da suka dauka. Za ka ga idan aka dauki lokaci sai ma'aurata ko Fadodi na mantawa ko kin cika alkawarin da suka dauka yadda ya kamata. Wani mai mota ya kai motarsa gareji, bakanike ya yi abinda ya saba ya yi mata juye, ya canza filta. Amma motar ba ta tashi. Ashe tana da matsala a cikin inji. Mu ma ya kamata mu rika tambayar kanmu sosai domin yin gyaran da ya kamata a rayuwar mu. Sabunta abubuwa kamar alkawari da muka dauka ya na muhimmanci sosai abu ne mai kyau.
Sabunta alkawarin da Fadodi dauka lokacin da aka nada a matsayin Firistocin Ikilisiyar Katolika. Mai girmama Bishop ne ya jagoranci wannan hidima.
Baiko (offertory). Kungiyar mawaka (Catholic choir) suka yi waka.
Kawo mayuka zuwa bagadin Ubangiji.
Emmanuela Adoyela - Mai domin marasa lafiya (Oil of the sick)
SSgt Cate. Umoh Thomas - Mai domin yin Baptisma (Oil of the Catechumen)
Rev. Fr. Nura Samaila Emmanuel - Mai domin yin Baptisma, nada Fadodi da Bishop, kebe Ikilisiya da bagadi wato 'dedication of the church and altar' (Sacred Crism).
Kawo burodi da wayin (Oblata)
Maida burodi da wayin su zama Jiki da Jinin Yesu na gaskiya (Consecration)
Albarkatar mai domin marasa lafiya
Lokacin karɓar Jiki da jinin Yesu (Cimar Ubangiji).
Albarkatar man Catechumen da Scared Crism daga Mai girma Bishop.
Kaddamar da Kwamitin Sadarwa (Communication Team) na Katsina Diocese daga Mai girma Bishop.
Sanarwai (Announcements)
An sanar da sabbin chaplains na wadansu kungiyoyi matakin Dayosis
An bada rahoton Cathedraticum da aka gudanar a kowanne Deneary a wannan diocese
Zumuntar mata na diocese
Ta bakin vocation director Rev. Fr. ya yi roko da kira ga jama'a domin a taimaka domin horas da seminarians, saboda yanzu muna semenirian guda 40. Ana ga mutum-mutum domin bada taimako.
Mai girmama Bishop ya yi godiya domin mutane da suka goyon baya. Ubangiji ya kai kowa gida lafiya. Amin.
Albarkar karshe daga Bishop
Wakar fita daga choir.